Kamfanin dillancin labaran Ahlul Baiti (ABNA) ya habarta cewa, an gudanar da bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (AS) a zauren majalissar Ahlulbaiti ta duniya. Ayatullah Ramezani ya halarci bikin, inda ya gabatar da jawabi inda ya taya murna na wannan taro mai albarka da kuma shigowar makon hadin kai. Ya godewa Jagoran bisa amincewar da ya yi masa tare da sake nada shi da kuma kara masa nauyin da ya rataya a wuyansa a Majalisar a matsayin Babban Sakatare. Ya ci gaba da cewa: "Bibiyan al'amuran 'yan Shi'a a duniya wani muhimmin aiki ne da aka damka wa majalisar Ahlulbaiti ta duniya, ina fatan ta hanyar daukar sabbin matakai, zan ci gaba da bin tafarkin kawo sauyi da ci gaba da kuma cimma manyan manufofin majalisar".

























Your Comment